Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Dubban 'yan Burkina Faso sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro

Dubban mutane a Burkina Faso sun gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar inda suke neman gwamnati ta dauki matakan kawo karshen hare-haren ta’addancin da suka addabi sassan kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga kan matsalar tsaro a Burkina Faso.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga kan matsalar tsaro a Burkina Faso. © Africanews / AFP
Talla

Zanga-zangar da ta gudana a birnin Ouagadougou na zuwa ne bayan kisan gillar da ‘yan ta’adda suka yiwa mutane fiye da 130 ranar 4 ga watan Yuni a garin Solhan dake arewacin kasar.

Karo na farko kenan da ‘yan adawa tare da hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula suka jagoranci zanga-zangar matsin lamba ga gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore, tun bayan nasarar tazarcen da yayi a zaben shekarar bara.

Tun daga shekarar 2015 al’ummar Burkina Faso suka soma fuskantar hare-haren ta’addancin kungiyoyi masu alaka da Al Qa’eda, tashin hankalin da kawo yanzu ya raba mutane akalla miliyan 1 da dubu 200 da muhallansu, yayin da wasu fiye da dubu 1 da 300 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.