Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Shugaban Burkina Faso ya kori ministoci 2 saboda tsaro

Shugaban Burkina Faso Roch March Christian Kabore ya tube ministan sojoji Cheriff Sy da kuma takwaransa na tsaron cikin gida Ousseni Compaore daga mukamansu, a matsayin ladaftarwa sakamakon kisan da ‘yan ta’adda suka yiwa fararen hula 132 a garin Solhan cikin watan jiya.

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore.
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore. © REUTERS/Fabrizio Bensch/File Photo
Talla

A yanzu dai shugaba Kabore ne da kansa zai rike mukamin ministan sojoji, yayin da Maxime Kone ya zama sabon ministan tsaron cikin gidan kasar.

A farkon watan Yuni hukumomin Burkina Faso suka ce mutane sama da dubu 7 sun tsere daga wasu yankunan kasar saboda rashin tsaro.

Fira Ministan Burkina Faso Christophe Dabire ne ya bayyana tserewar mutanen sama da 7,000 zuwa wasu yankunan domin samun mafaka bayan ya ziyarci yankin da Yan bindiga suka kashe mutane sama da 130 a farkon watan Yuni.

Akalla mutane 138 da suka hada da mata da maza da yara kanana ‘yan bindigar suka kashe a kauyen Solhan yayin da wasu kusan 40 suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.