Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

'Yan ta'adda sun yi wa sama da mutane 100 kisan gilla a Burkina Faso

Wasu wadanda ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne sun yi wa akalla fararen hula 114 kisan gilla a arewacin Burkina Faso biyon bayan hari mafi muni tun da rikicin masu ikirarin jihadi ya barke  a kasar a shekarar 2015, kamar yadda hukumomi suka sanar a yau Asabar.

Taswirar Burkina Faso da ke nuni da arewacin kasar.
Taswirar Burkina Faso da ke nuni da arewacin kasar. RFI
Talla

Shugab Roch Marc Christian Kabore ya yi tir da harin na kusa d iyakokin da Mali da Nijar, inda mayaka masu alaka da kungiyoyin al Qaeda da IS ke ta kai fararen hula hare hare.

Majiyoyin tsaro sun ce harin  mafi muni ya auku ne a daren Juma’a zuwa wayewar garin Asabar, lokacin da wasu masu dauke da makamai suka kai samame yankin Solhan.

Wadanda suka mutu sun hada da mata da maza masu mabanbantan shekaru, kuma gwamnati ta tabbatar da adadin mamatan.

Da misalin karfe 2 na daren Juma’a ne maharan suka kaddamar da hari a kan sansanin mayakan sa kai da ke taimaka wa sojojin kasar wajen yaki da ‘yan ta’adda, kafin daga bisani suka fara bi gida gida suna kashe mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.