Isa ga babban shafi
Burkina-Ta'addanci

Harin ta'addanci ya hallaka mutane 9 a Burkina Faso

Majiyoyin tsaro a Burkina Faso sun tabbatar da kisan mutum 9 a wasu hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi da suka faru a yankin arewacin kasar mai fama da rikici.

Hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da haddasa asarar dimbin rayuka a Burkina Faso.
Hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da haddasa asarar dimbin rayuka a Burkina Faso. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Majiyar tsaron ta Burkina Faso ta ce cikin wadanda harin ya hallaka har da shugaban gargajiya a wani kauye da ke dab da garin Pissila baya ga wasu Sojin sa kai 3 yayinda wasu mutane 3 kuma suka bace har zuwa yanzu ba a san inda su ke ba.

Sai dai majiyar wadda ke shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa, yadda harin ya faru ta ce nan ta ke aka kashe ilahirin maharan da suka kaddamar da farmakin ba tare da bayyana adadinsu ba.

Majiyar ta ce harin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren lahadi dai dai lokacin da al’ummar kauyen tare da sojojin sa kai ke wani taron tsara yadda za su tunkari matsalolin tsaron da suka addabesu.

Rahotanni sun ce a ‘yan kwanakin baya-bayan nan, daruruwan mutane ke tserewa daga kauyukansu zuwa cikin garin an Pissila don samun tsaro bayan tsanantar hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Galibin Sojojin sa kai da ke cikin kungiyar VDF mai rajin kare al’ummar yankin dai na samu cikakken horo daga rundunar Sojin Burkina Faso gabanin fara artabu da mayakan masu ikirarin jihadi, inda zuwa yanzu aka kashe musu mutane fiye da 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.