Isa ga babban shafi

Guterres ya bayyana kaduwar sa da kisan Burkina Faso

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana matukar kaduwar sa da kashe fararen hula sama da 130 da Yan ta'adda suka yi a kasar Burkina Faso wanda shine mafi muni tun daga shekarar 2015.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres AP - Maxim Shemetov
Talla

Gwamnatin Burkina Faso tace Yan ta’addan da suka aikata kisan sun kai hari ne cikin dare inda suka cinna wuta a gidaje da kuma kasuwar kauyen Yagha dake ci cikin dare a kusa da iyakar Mali da Jamhuriyar Nijar.

Bayan Allah-wadai da kazamin harin Guterres ya bayyana muhimmancin taimakawa kasashen duniya yaki da tsatsauran ra’ayi.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cikaken goyan bayan ta ga hukumomin Burkina Faso a shirin da suke yin a magance wannan barazanar da kuma tabbatar da zaman lafia a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.