Isa ga babban shafi
AFRIKA-TSARO

Amurka ta bayyana damuwa kan sanya kananan yara aikin soji

Kasar Amurka tace akasarin Yan bindigar da suka kashe fararen hula a Burkina Faso a cikin wannan watan yara ne kanana, abinda ya sa ta bukaci daukar mataki mai karfi akan masu amfani da yara a matsayin soji.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres Fabrice COFFRINI AFP/File
Talla

Jakadaiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta bayyana haka lokacin da ake gudanar da taron shugabannin kasashen dake da kujera a kwamitin sulhu akan amfani da yara a wajen tashin hankali.

Thomas-Greenfield tace irin wadannan yaran zasu shaida maka labarin da baka taba ji ba da ya kunshi yadda ake amfani da karfi wajen tirsasa musu daukar makami da aikata kisa da ma kashe iyayen su da ‘yan uwan su.

Jakadiyar tace wani lokaci tsayin wadannan yaran da ake amfani da su bai ma wuce na bindigar da suke dauke da shi ba, amma sai ka ga ana sa su aikata kisa da kuma iakata laifuffukan yaki.

A ranar 5 ga watan Yunin da muke ciki wata kungiyar Yan bindiga ta kai hari a kauyen Solhan dake Burkina Faso kusa da iyakokin Mali da Jamhuriyar Nijar inda ta kashe mutane 132, a hari mafi muni da aka taba gani tunda daga shekarar 2015.

Mazauna yankin sun ce adadin mutanen da suka mutu lokacin harin ya kai 160 kuma cikin su harda yara 20.

Kakakin gwamnatin Burkina Faso Ousseni Tamboura ya tabbatar da cewar cikin maharani harda yara kanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.