Isa ga babban shafi
Libya

An gano wani kabari mai dauke da gawarwakin mutane 10 a Libya

Masu Bincike a kasar Libya sun gano wani kabari mai dauke da gawarwakin mutane 10 a Yankin da Yan Tawaye ke iko da shi a wajen binin Tripoli.

Wani sojin Libya tsaya a inda aka gano makeken kabari dauke da mutane 10
Wani sojin Libya tsaya a inda aka gano makeken kabari dauke da mutane 10 REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Gwamnatin hadin kan kasar tace, 3 daga cikin gawarwakin an rufe fuskokin su kafin kashe su a Tarhuna dake da nisan kilimowa 80 daga babban birnin kasar.

Majalisar Dinkin Duniay ta bayyana matukar damuwa kan lokacin da aka gano irin wadannan kaburbura masu dauke da mutane da dama a watan Yunin bara bayan janyewar da dakarun Khalifa Haftar suka yi.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tace akalla mutane sama da 300 suka bata a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.