Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Wanene zai yi nasarar lashe zaben Jamhuriyar Congo?

Al’ummar Jamhuriyar Congo na kada kuri’a a zaben shugaban kasar, wanda ake sa ran a karon farko, zai bada damar mika mulki cikin ruwan sanyi, tun bayan ‘yan cin da kasar ta samu daga Belgium a shekarar 1960.

Daya daga cikin rumfunan zabe a garin Goma da ke Jamhuriyar Congo bayan soma kada kuri'a a zaben shugaban kasar. 30/12/2018.
Daya daga cikin rumfunan zabe a garin Goma da ke Jamhuriyar Congo bayan soma kada kuri'a a zaben shugaban kasar. 30/12/2018. PATRICK MEINHARDT / AFP
Talla

‘Yan takara 21 ke fafatawa a zaben na yau, wanda ke gudana tare da na ‘yan majalisu da kananan hukumomi.

Zaben na gudana yayin da ‘yan adawa ke zargin shugaba Joseph Kabila zai tafka magudi domin baiwa dan takararsa Shadary mulki, sai kuma fargabar barkewar rikici bayan zaben.

A ranar Asabar dai manyan ‘yan takara biyu na bangarorin ‘yan adawa, Martin Fayulu da Felix Tshisekedi sun ki sa hannu kan alkawarin kaucewa haddasa rikici idan basu gamsu da sakamakon zaben ba.

Wata kuri’ar jin ra’ayi da wata cibiyar sa ido kan siyasar Jamhuriyar Congo ta gudanar mai hedikwata a New York, ta nuna cewa jagoran ‘yan adawa Martin Fayulu ke kan gaba wajen farin jini tsakanin 'yan takara da yawan magoya baya kashi 44, sai kuma Tshisekedi mai kashi 24, yayin da Shadary, dan takarar shugaba Joseph Kabila ke da kashi 18.

Zalika sakamakon kuri’ar ra’ayin ya nuna cewa, tsakanin kashi 43 zuwa 53 na ‘yan kasar sun ce ba za su amince da sakamakon zaben ba, muddin dan takarar shugaba Kabila ne yayi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.