Isa ga babban shafi
DRC

An jinkirta zabe a yankunan 'yan adawa a Congo

Hukumar Zaben Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta ce, za ta jinkirta gudanar da zaben shugabacin kasar da na ‘yan majalisu a wasu birane uku na 'yan adawa har sai nan da watan Mayu, abin da ke nufin cewa, ba za a yi la’akari da kuri’un wadannan birane ba a zaben ranar Lahadi mai zuwa.

Shugaban Hukumar Zaben Jamhuriyar Congo, Corneille Nangaa, a taron manema labarai
Shugaban Hukumar Zaben Jamhuriyar Congo, Corneille Nangaa, a taron manema labarai ISSOUF SANOGO, Luis TATO / AFP
Talla

Biranen da wannan mataki ya shafa sun hada da Beni da Butembo da ke fafutukar magance annubar Ebola wadda ta sake afka musu a cikin watan Agusta, sai kuma birnin Yumbi wanda shi kuma ya yi fama da rikicin kabilancin da ya lakume rayukan mutane 100 a makon jiya.

Tuni shugabannin ‘yan adawa suka bukaci gudanar da zanga-zanga lura da cewa, matakin jinkirta zaben ya takaita ne a wuraren da suka fi yawan magoya baya.

Kasashen duniya sun zura ido domin ganin irin sahihin zaben da za a gudanar a Jamhuriyar Demokradiyar Congo wadda ta yi fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.