Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An rufe kashi 20 cikin 100 na rumfunan zabe a Kinshasa

Hukumar zaben Jamhuriyar Congo, ta ce ba za a bude kashi 20 cikin 100, na rumfunan zaben da ke birnin Kinshasa ba, yayin zaben shugaban kasar da zai gudana a gobe Lahadi.

Wasu masu zanga-zanga a babban birnin Jamhuriyar Congo, Kinshasa.
Wasu masu zanga-zanga a babban birnin Jamhuriyar Congo, Kinshasa. AFP
Talla

A cewar hukumar zaben jimillar rumfunan da baza’a bude ba sun kai dubu 1,600 daga cikin dubu 7,939, sai dai za’a rarraba wadanda lamarin ya shafa zuwa wasu rumfunan domin kada kuri’unsu.

Hukumar zaben CENI, ta ce tilas ta dauki matakin, a dalilin gobarar da ta kone injinan zabe akalla dubu 8,000 daga cikin dubu 10,368 da ya kamata a yi amfani da su a birnin na Kinshasa.

Sai dai ‘yan adawa sun bayyana matakin, a matsayin wata sabuwar dabarar murda sakamakon zabe, ta hanyar haramtawa ‘yan kasar da dama, zabar ra’ayinsu.

A cewar bangaren ‘yan adawa akwai lauje cikin nadi, la’akari da yadda hukumar zaben ta yi amai ta lashe kan yankunan Beni da Butumbo masu fama da cutar Ebola, da ta ce sai a watan Maris mai zuwa zabe zai gudana a yankunan, sabanin yadda a baya ta sha alwashin gudanar da zabuka a yankunan kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.