Isa ga babban shafi
Kenya

An kama wasu jami'an hukumar bautawa kasar Kenya

Gwamnatin Kenya ta bayar da umurnin gudanar da bincike a kan wasu bankunan kasar 10 da ake zargi da boye kudaden da yawansu ya kai dala milyan 100 da wasu manyan jami’an hukumar aikin bautawa kasar suka kwashe.

Masu zanga-zanga  a kasar Kenya
Masu zanga-zanga a kasar Kenya REUTERS/Baz Ratner
Talla

Matakin gudanar da bincike a kan bankunan ya biyo bayan cafke wasu manyan jami’an hukumar bautawa kasar ne da aka cafke kan zargin su da hannu a wannan almundahna.

Rahotanni sun bayyana sunayen bankuna 9, da wata ƙungiyar hadin gwiwa ta kudi, a matsayin cibiyoyin da jamian yan sanda da kuma masu bincike a babban bankin kasar zasu bincika.

Masu bada rancen kudin sun hada da Babbar cibiyar samar da rancen kadarori ta kasar kenya, kampanin KCB, da kuma Ƙungiyar Amincin Ƙididdiga ta Kamfanin Kenya.

Darektan binciken laifuka, George Kinoti, ya shaidawa manema labarai cewa adadin wadanda aka zarga da aikata laifin dai-dai ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.