Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai bar Abuja zuwa Amurka a gobe asabar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai bar gida a gobe Asabar zuwa birnin Washington DC na Amurka don amsa gayyatar shugaban Amurka Donald Trump.Ziyarar ta Muhammadu Buhari na zuwa ne kwanaki kalilan bayan dawowa daga makamanciyar ta a birnin London.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. RFIHausa/Kabiru Yusuf
Talla

Sanarwar da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar ta ce Buharin zai yi mabanbantan zama da Donald Trump a ranar litinin.

A cewar sanarwar dukkanin tattaunawar shugaannin biyu za ta mayar da hankali ne kan al’amuran da suka shafi inganta tsaro tattalin arziki da kuma karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta ce bayan ganawar Buharin da Donald Trump zai kuma gana da wata tawagar kwararru kan harkokin noma da kiwo da kuma ‘yan kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.