Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan majalisa sun soki Buhari bisa biyan kudaden makamai ga Amurka

Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan Najeriya, sun nuna bacin ransu akan matakin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dauka, na rashin neman amincewarsu kafin biyan dala miliyan 496 na kudaden jiragen yaki da makamai da Najeriya ta saya daga Amurka.

Zauren majalisar wakilan Najeriya.
Zauren majalisar wakilan Najeriya. Stringer/Reuters
Talla

‘Yan majalisar wakilan sun bayyana cewa aikata laifin da shugaba Buhari ya yi, ya cancanci a dauki matakin tsigewa a kanshi.

Cikin wasikar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa zauren majalisar wakilan, ya bayyana cewa, ya dauki matakin biyan kudaden kai tsaye ne, bisa fata ko tsammanin cewa ‘yan majalisar zasu goyi bayan matakin ba tare da kawowa shirin cikas ba.

Tuni dai Amurka ta tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta biya kudaden jiragen yakin kirar Super Tucano da sauran makaman da suka cimma yarjejeniyar saidawa Najeriya domin yakar kungiyar Boko Haram, da sauran ayyukan ta’addanci.

Sai dai wadannan jiragen yakin da makaman ba zasu isa hannun Najeriya ba sai a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.