Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sanar da dalilinsa na tsayawa takara a 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da ya sa ya bayyana aniyar sa ta takarar zaben shekara mai zuwa. Yayin ganawa da Arch Bishop na Cantebury Justin Welby a London, Buhari ya ce ya bayyana takarar ta sa ce, domin kawo karshen cece kucen da ake tayi a Najeriya.

Buhari ya alakanta kwararowar 'yan ta'adda zuwa sassa daban daban na Afrika da tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi.
Buhari ya alakanta kwararowar 'yan ta'adda zuwa sassa daban daban na Afrika da tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi. REUTERS/Dan Kitwood
Talla

Muhammadu Buhari ya ce har yanzu akwai batutuwa da dama da suka hadar da matsalar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da tattalin arziki da kuma noma da ya dace su dora ginin da suka dauko, wajen inganta Najeriya.

Dangane da rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma, Buhari ya ce wannan matsalar ta girme musu, amma kuma yanzu matsalar ta karu ne saboda kwararowar mutanen da ke dauke da makamai daga Sahel zuwa kasashen Afirka ta Yamma.

Buhari ya ce akasarin wadannan mutane tsohon shugaban Libya Muammar Ghadafi ya horar da su ya kuma basu makamai, yayin da mutuwar sa ya sa su suka fantsama zuwa kasashe da dama.

Dangane da Leah Sharibu da ke hannun kungiyar boko haram, shugaban Najeriyar ya ce suna bin lamarin ta karkashin kasa kuma suna fatar ganin an sako ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.