Isa ga babban shafi
Amurka-Ghana

Yan adawa sun soki yarjejeniyar baiwa sojin Amurka damar shiga Ghana

J’amiyyar NPP mai mulkin Ghana tayi Allah wadai da kalaman wani jigon dan adawar kasar na kiran yi juyin mulki saboda yarjejeniyar baiwa sojin Amurka damar girke dakarun su a kasar.

Nana Akufo-Addo  Shugaban kasar Ghana
Nana Akufo-Addo Shugaban kasar Ghana REUTERS/Luc Gnago
Talla

Ministan yada labarai Mustapha Abdulhameed yayi Allah wadai da kalaman, inda ya bukaci yan siyasa su dinga mutunta tanade tanaden demokradiya.

An ruwaito Mataimakin Sakatare Janar na Jam’iyyar NDC, Koku Anyidoho na bayyana cewar za’a samu bore ga gwamnatin kasar da kuma juyin juya hali sakamakon kulla yarjejeniyar wadda zata baiwa sojin Amurka damar shiga kasar ba tare da biyan haraji ba da kuma shiga duk inda suke so.

 A cikin makon da ya gabata dai ne Majalisar Ghana ta amince da bai wa Amurka damar girke sojojinta a kasar, kudurin da bai samu amincewar ‘yan adawa a zauren majalisar ba, wadanda suka kaurcewa kada kuri’a a kansa.

Ana saran gudanar da zanga zanga a wasu biranen kasar ta Ghana kan yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.