Isa ga babban shafi
Sudan

MDD na binciken dakarun Ghana a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bincike kan zargin cin zarafin mata da ake yi wa 'yan Sandan kasar Ghana da ke aikin samar da tsaro a  Sudan ta Kudu.

Daniel Finnan
Talla

Majalisar ta ce ta umurci 'yan Sandan 46 da ke aiki a garin Wau da ke arewa maso yammacin Juba da su koma cikin Juba domin bada damar gudanar da bincike a sansanin 'yan gudun hijirar da suke aiki.

Sanarwar Majalisar ta ce, David Shearer, jami’in da ke kula da ayyukan samar da zaman lafiyar ya kadu da zargin cewar, 'yan sandan na biyan mata domin yin lalata da su a sansanin.

Akalla 'yan sanda 1,500 ke aiki cikin rundunar da ke dauke da jami’an tsaro 17,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.