An girke dubban 'yan sandan Jamhuriyar Congo a Kinshasa
Dubban jami’an ‘yan sandan Jamhuriyar Congo aka girke a sassan babban birnin kasar Kinshasa, a dai dai lokacin da a yau ‘yan adawa suka shirya gudanar da zanga-zangar tilastawa Joseph Kabila sauka daga shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Limaman Cocin Katolika na kasar ne suka bukaci sake fita zanga-zangar duka da haramta ta da gwamnati ta yi, makwanni uku bayan da makamanciyar zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma, inda akalla mutane 12 suka hallaka.
Kiran limaman Cocin, ya samu goyon bayan shugabancin mabiya addinin Islama da ke kasar, kamar yadda wakilinsu Shiekh Ali Mwinyi M’Kuu ya tabbatar.
Tun a jiya Asabar ‘yan sandan kasar suka kafa shingayen bincike a sassan birnin na Kinshasa, domin zakulo masu dauke da makamai, da kuma shirin dakile gudanar da zanga-zanar da gwamnatin Kabila ta haramta gudanar da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu