Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron Jamhuriyar Congo sun tarwatsa taron malaman Coci

‘Yan sandan Jamhuriyar Congo sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa jerin gwanon daruruwan, malaman Coci, da suka taru a babban birnin kasar Kinshasa, domin zaman makokin mutanen da suka rasa rayukansu, a zanga-zangar neman shugaban kasar, Joseph Kabila ya yi murabus.

Jami'an tsaron Jamhuriyar Congo sun harba hayaki mai sa hawaye kan malaman Coci masu zanga-zanga.
Jami'an tsaron Jamhuriyar Congo sun harba hayaki mai sa hawaye kan malaman Coci masu zanga-zanga. SundiataPost
Talla

Kamfanin dillancin labarai Reuters, ya rawaito cewa, jami’an tsaron sun dauki matakin ne domin dakile yiwuwar juyewar taron zuwa wata sabuwar, zanga-zanga.

Shugaban mabiya darikar Roman Katolika na kasar ta Congo, pierrot Mwanamputu, ya yi alla wadai da matakin tarwatsa jerin gwanon manbobin nasa, inda ya ce rashin sanin hakkin dan adam ne ya jawo hakan.

‘Yan kasar Jamhuriyar Congo masu yawan gaske ne suka rasa rayukansu cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon zanga-zangar da suke ci gaba da yi domin tilastawa shugaban kasar Joseph Kabila sauka daga mukaminsa, bayan da wa’adinsa ya kare.

Zalika matsalar yawaitar samun kazamin fada, da kuma hare-haren mayakan ‘yan tawaye, ya sake jefa ‘yan kasar cikin munin yanayi, tare da tilastawa dubbai tserewa daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.