Isa ga babban shafi
Mali

Amadou Toumani Toure ya koma kasar Mali

Tsohon shugaban Mali wanda sojoji suka kifar, Amadou Toumani Toure ya koma kasar a jiya lahadi bayan share sama da shekaru 5 a kasar Senegal, inda ya samu gagarumin tarbo daga al’ummar kasar da kuma shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Amadou Touani Touré tsohon Shugaban kasar Mali
Amadou Touani Touré tsohon Shugaban kasar Mali AFP/Michele Cattani
Talla

Idan aka yi tuni hambararren Shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure ya yi murabus daga mukamin shi na shugaban kasa karkashin yarjejeniyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS domin kawo karshen rikicin kasar bayan Sojoji sun kifar da gwamnatinsa.

Yarjejeniyar kuma ta amince da dage takunkumin da aka kakabawa kasar Mali tare da yin afuwa ga Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Toure.

Bayan saukarsa a filin jiragen sama na Bamako, Amadou Toumani Toure ya wuce zuwa gidan shugaban kasar mai-ci inda aka shirya masa liyafar cin abinci, kuma a wannan lokaci ne ya bayyana farin cikinsa dangane da dawowarsa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.