Rundunar Faransa ta kashe 'yan ta’adda a kan iyakar Mali da Algeria
Rundunar Sojin Faransa ta sanar da kashe wasu ‘yan ta’adda 15 a kan iyakar Mali da Algeria a ci gaba da farautar masu ta da kayar baya a Yankin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Faransa ya ce an kai harin ne daren litinin a Yankin Abeibara kan ‘ya’yan kungiyar Ansaruddine.
Bayanai sun ce anyi amfani da jiragen saman yaki da jirage masu saukar ungulu da kuma sojojin kasa wajen kai harin.
Babu dai Karin haske ko harin na da nasaba da kisan da aka yiwa sojojin Amurka da Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu