Isa ga babban shafi
Yankin Sahel

Nijar da Mali na neman taimako kan yaki da ta'addanci

Kasashen Nijar da Mali sun bukaci kasashen duniya da su taimaka wajen bada kudaden da za a tafiyar da rundunar yaki da 'yan ta’adda a Yankin Sahel.

Shugabannin kasashen yankin Sahel da ke kokarin yaki da ta'addanci
Shugabannin kasashen yankin Sahel da ke kokarin yaki da ta'addanci AFP PHOTO/AHMED OULD MOHAMED OULD ELHADJ
Talla

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Muhammadou Issofou sun ce, dakarun da kasashen Mali da Mauritania da Burkina Faso da Nijar da Chadi suka girke nada matukar tasiri wajen murkushe 'yan ta’addan da suka addabi yankin.

Shugaba Issoufou ya ce, dakarun ba wai za su kare mutanen kadai ba ne,  har ma da na duniya baki daya, domin dan ta’adda bai san iyakar wata kasa ba.

Shugaban ya bayyana gagarumar nasarar da irin wannan hadakar dakarun da ke yaki da Boko Haram ta samu, in da yake cewar, kasashen 5 ba su da isassun kudaden tafiyar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.