Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya kori mataimakinsa

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, ya kori mataimakinsa, Emmerson Mnangagwa, a wani yanayi da ake ganin sharar fage ce, ya yi wa matarsa.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe tare da uwargidansa Grace Mugabe yayinda suke halartar taron jam'iyyarsu ta ZANU (PF) a Chinhoyi, da ke Zimbabwe, ranar 29 ga watan Yuli da ya gabata.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe tare da uwargidansa Grace Mugabe yayinda suke halartar taron jam'iyyarsu ta ZANU (PF) a Chinhoyi, da ke Zimbabwe, ranar 29 ga watan Yuli da ya gabata. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Matakin ya zo ne bayanda dagantaka ta yi tsami tsakanin mai dakin Mugaben wato Grace, mataimakinsa, wadanda ake sa ran daga cikinsu ne za’a samu wanda zai maye gurbinsa

Yayinda yake sanar da tube Mnangagwa daga mukaminsa, Ministan yada labaran kasar ta Zaimbabwe Khaya Moyo, ya ce mataimakin shugaban kasar ya dade yana aikata laifuka da dama da suka hada da cin amana da kuma haddasa rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki.

Tun a ranar Asabar da ta gabata Robert Mugabe yayi barazanar korar mataimakinnasa, bisa zargin da yake masa na neman mamaye harkokin a jam’iyyar mai mulki ta Zanu PF.

Har yanzu dai babu wanda sunan wanda aka bayyana da zai maye gurbin Emmerson Mnangagwa, sai dai Phelekezela Mphoko na nan a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.