Mutane 11 suka mutu, Fursunoni 900 suka tsere a Janhuriyar Democradiya ta Congo
A kasar Janhuriyar Democradiya ta Congo mutane akalla 11 suka mutu, fursunoni fiye da 900 kuma suka tsere daga wani gidan yari dake gabashin kasar a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kaiwa gidan yarin farmaki yau Lahadi.
Wallafawa ranar:
Gwamnan yankin Arewacin gunduman Kivu inda gidan yarin na garin Kangwayi yake, wato Julien Paluku ya shaidawa manema labarai cewa da rana tsaka ‘yan bindiga suka dirawwa gidan yarin.
A cewar shi a musayar wuta tsakanin ‘yan bindigan da jami'an tsaro dake gadin gidan yarin ne aka sami gawa 11 nan take.
A yanzu haka ya ce gidan yarin mai mutane 966, abinda suka rage basu wuce 30 ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu