Isa ga babban shafi
Benin

Ana cece-kuce kan lafiyar shugaban Jamhuriyyar Benin

Mafi yawa daga cikin al’ummar Jamhuriyar Benin na ci gaba da diga ayar tambaya game da halin da shugaban kasar Patrice Talon ke ciki, bayan da rahotonni suka ce ya share tsawon mako daya yana jinya a wani asibiti da ke Faransa.

Shugaban Bénin Patrice Talon
Shugaban Bénin Patrice Talon THIERRY CHARLIER / AFP
Talla

Shugaba Talon ya fice daga kasar ne ba tare da sanar da ‘yan kasar ba, kafin daga bisani ministan harkokin wajen kasar Aurelien Agbenonci ya ce ya tafi hutu ne, kuma zai yi amfani da damar ne domin duba lafiyarsa.

Kwanakin da shugaban ya kwashe ba ya cikin kasar ya janyo cece-kuce a Benin, musamman kan rashin lafiyarsa.

Talon dai ya kauracewa taron majalisar ministocinsa da kuma taron kasashen yammacin Afrika ECOWAS da aka gudanar a Liberia a ranar 4 ga Yuni.

Wata majiya daga fadar gwamnatin Benin ta ce shugaban na kan hanyar dawo wa kasar a makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.