Mali
An shawarci gwamnatin Mali da ta tattauna da kungiyoyin jihadi
Taron hada kan kasa da aka gudanar a Mali ya bukaci gwamnatin kasar ta shiga tattaunawa da kungiyoyin da ke kiransu masu Jihadi domin samar da zaman lafiya a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Taron wanda aka kammala a jiya, ya shawarci gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita da ta tattauna da kungiyar Ansarud Dine ta Iyag Ag Ghali da kuma wata kungiyar da ke karkashin jagorancin wani malami mai suna Amadou Koufa, kungiyoyin da suka sha kai hare-hare tare da kashe dimbin jama’a a kasar ta Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu