Isa ga babban shafi
Jamus-Afrika

Jamus zata karfafa ayyukan sojinta a Mali

Gwamnatin kasar Jamus na shirin karfafa dakarun Majalisar dinkin Duniya dake aikin samar da zaman lafiya a Mali wajen samar musu jiragen da zasu dinga tattara bayanan asiri.

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Matakin ya biyo bayan karuwar hare haren da ake samu a Yankin Gao na kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Jamus Kanar Simone Gruen, tace suna bukatar irin jiragen da Amurka ke amfani da su a kasar Afghanistan wajen tattara bayanan sirri.

Dakarun dake aikin samar da zaman lafiya a Mali na cigaba da fuskantar hadurra ciki harda harin kunar bakin waken da ya kashe mutane 77 a watan jiya wanda kungiyar dake alaka da Al Qaeda ta dauki alhaki.

Kasar Jamus na shirin kara yawan dakarunta dake Mali a cikin wannan shekara tare da jiragen saman masu saukar ungulu dake kai hari guda 8 da kuma sojoji 350.

Yanzu haka sojojin Majalisar Dinkin Duniya 15,000 ke aiki a Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.