Isa ga babban shafi
Mali

Mali: ‘Yan tawaye da ‘yan adawa za su kauracewa taron kasa

Gwamnatin Mali ta ce taron kasa da ta shirya na fahimtar juna na nan kamar yadda aka shirya a gobe litinin duk da wani bangare na jam'iyyun adawa da kuma ‘yan tawayen kasar sun ce zasu kauracewa taron.

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita Pierre Rene-Worms/RFI
Talla

Gwamnatin Mali tace ta shirya wa taron wanda Za a share tsawon mako daya ana gudanarwa daga gobe Litinin zuwa 2 ga Afrilu.

Amma wasu jam’iyyun adawa da ‘yan tawayen sun ce zasu kauracewa taron wanda aka shirya karkashin yarjejeniyar da aka cim ma a Algiers a 2015.

Amma bangaren ‘yan tawayen MAA da ke fafutikar kafa kasar Azawad sun ce zasu ahalarci taron.

Taron na fahimtar juna ya shafi yin muhawara game da rikicin kasar tsakanin bangarori da dama da nufin sasantawa da kuma zaman lafiya.

Wasu jam’iyyun adawa na son a shafe makwanni ana taron maimakon mako guda.

A shekarar 2012 ne ‘yan tawaye suka kwace ikon arewacin Mali, kafin dakarun Faransa fatattake su a 2013.

Amma har yanzu an kasa wanzar da zaman lafiya a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.