Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta fara bincike kan kisan da aka yiwa sojinta a bariki

Gwamnatin Kasar Mali tace ta kaddamar da bincike kan kisan da aka yiwa wasu sojojin kasar 11 a barikin su dake kusa da iyakar Burkina Faso, yayin da sojojin yan tawaye suka yiwa garin Timbuktu kawanya.

Wasu dakarun Mali hade da tsaffin 'yan tawaye da ke gudanar da sintirin hadin gwiwa
Wasu dakarun Mali hade da tsaffin 'yan tawaye da ke gudanar da sintirin hadin gwiwa AFP
Talla

Majiyar sojin kasar ta tabbatar da kisan sojojin 11, a kauyen Boulekssi dake kan iyaka jiya lahadi, lokacin da wasu ‘yan tawayen suka kai hari.

Sojojin Faransa dake kasar, sun kai musu dauki da jiragen sama masu saukar ungulu, yayin da wasu sojojin gwamnati 20 suka tsallaka zuwa Burkina dan kaucewa harin.

Idan ba’a manta ba dai a shekarar 2012 yankin arewacin Mali ya fada hannun ‘yan tawayen Mali da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda, to sai dai a watan Janairu na shekara ta 2013 sojin Faransa suka jagoranci kwato yankin daga mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.