Italiya ta kulla yarjejeniya da shugabanin kabilun Libya
Gwamnatin Italiya ta ce ta kulla yarjejeniya da shugabanin wasu kabilun dake adawa da juna a kudacin Libya dan samar da tsaron da zai dakile kwararar baki ta kasar zuwa Turai.
Wallafawa ranar:
Ministan harkokin cikin gida Marco Minniti ya ce shugabanin kabilun 60 da suka hada da Abzinawa da Tubawa da kuma Larabawa sun amince da kudirori 12 bayan kwashe sa’oi 72 ana tattaunawa a asirce.
Ministan ya ce jami’an tsaron dake kula da iyaka za su dinga sintiri kan iyakar Libya mai nisan kilomita 5,000 a Kudancin kasar.
Kasar Libya ta zama wata babbar hanyar tsallakawa zuwa Turai tun bayan kauda shugaba Muamar Ghadafi daga karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu