Isa ga babban shafi
Turai-Afrika

"Mai yiwuwa a samu karin kwararar bakin haure a turai"-EU

Kungiyar kasashen Turai na kara yawan tallafin da take baiwa Libya da kuma horar da jami’anta, hadi da gina wasu sansanoni a sassan nahiyar Afirka domin dakile yawan bakin da ke kwarara Turai.

Fafaroma Francis yayin gaisawa da 'yan gudun hijira da ke sansanin Moria a tsibirin Lesbos na kasar Girka.
Fafaroma Francis yayin gaisawa da 'yan gudun hijira da ke sansanin Moria a tsibirin Lesbos na kasar Girka. Reuters/路透社
Talla

Kungiyar ta bayyana fargabar cewa mai yiwuwa a samu karuwar baki masu tafiya Turan, muddin aka kasa daukan matakan da suka dace.

Akalla baki 181,000 suka bi ta Libya zuwa Turai a shekara ta 2016, kuma daga cikinsu akwai yara kanana akalla 25,000.

Wani abin tada hankali shi ne yadda kananan yaran basu da masu kula da su, yayin da akalla sama da 5,000 suka mutu a teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.