Yarjejeniyar zaman lafiya za ta soma aiki a Mali
A ranar asabar mai zuwa ne sabbin hukumomin rikon kwarya za su fara aiki a yankunan arewacin kasar Mali, wannan dai na daga cikin muhimman batutuwan da ke kunshe a yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin gwamnati da kuma kungiyoyin ‘yan tawayen kasar.
Wallafawa ranar:
A yanzu dai an nada Shugaban kungiyar ‘yan tawayen yankin Azawad Hassan Ag Fagaga a matsayin gwamnan lardin Kidal.
Kasar Mali ta dadde tana fama da tashe tashen hankula sakamakon sabani a tsakanin bangaren gwamnati da kungiyoyin ‘yan tawaye hakan ya kuma haifar da rikicin da ke kai ga rasa rayuka da kuma hana zaman lafiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu