Isa ga babban shafi
Mali

An kashe mutane 13 a fadan kabilanci a Mali

Akalla mutane 13 suka mutu sakamakon wani fadan kabilanci tsakanin 'yan kabilar Fulani da Bambara a kasar Mali.

Fulani makiyaya da kabilar Bambara kuma manoma ne ke rikici da junan a Mali
Fulani makiyaya da kabilar Bambara kuma manoma ne ke rikici da junan a Mali REUTERS/via Reuters TV TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Ma’aikatar cikin gida ta tabbatar da tashin hankalin, yayin da wata majiya ta ce adadin ya kai 45.

Rahotanni sun ce fadan ya barke ne sakamakon kashe wani dan kabilar Bambara da ke da shagon sayar da kayan masarufi a wani gari da ke kusa da Macina, mai nisan kilomita 300 daga Bamako, abinda ya sa yan uwan sa suka dauki makamai dan daukar fan sa.

Su dai Fulani makiyaya ne a kasar yayin da 'Yan kabilar Bambara kuma manoma ne.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun barkewar irin wannan rikicin ba. A shekarar da ta gabata kungiyar kare hakkin dan Adam ta HRW ta janyo hankali da gargadi kan matakan dai-daita bangarorin da zaman lafiya ke gagarar su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.