Isa ga babban shafi
Mali

Ana bi gida gida domin gano Bafaransar da aka sace a Mali

Jami’an tsaron kasar Mali na ci gaba da bincike gida-gida a birnin Gao da ke arewacin kasar, domin gano wata Bafaransa mai suna Sophie Petronin, da aka sace tun ranar lahadin da ta gabata.

Sojojin Mali da ke aikin wanzar da tsawo a yankin Gao.
Sojojin Mali da ke aikin wanzar da tsawo a yankin Gao. RFI/David Baché
Talla

Har yanzu dai ba wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin sace ma’aikaciyar agajin da ta share tsawon shekaru fiye da 20 tana ayyukan jinkai a yankin na arewacin Mali.

A zantawar shi da RFI, Seydou Toure gwamnan lardin Gao ya bukaci jama’a su taimaka wa jami’an tsaro domin samun bayanan da za su bayar da damar gano maharan da kuma ‘yantar da Bafaransar.

Mista Toure ya ce Gao yankin ne da kusan kowa ya san kowa, saboda haka Sophie sananniya ce a cikin al’umma.

Sai dai kuma gwamnan ya ce akwai alamun maharani sun tsallako ne daga wani yanki suka yi awon gaba da ma’aikaciyar agajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.