An fara shari’ar Amadou Sanogo na Mali
An soma shari’ar Kaftin Amadou Sanogo a ranar Laraba wanda ya jagorancin juyin mulkin 2012 tare da jefa kasar cikin rikici. Ana tuhumarsa ne da kisan sojojin da suka bijere wa jagorancin shi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An cafke Janar Sanago ne bayan tuhumarsa da sace wasu Sojoji tare kashe su wadanda suka ki ba shi goyon bayan hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.
Juyin mulkin da Janar Sanogo ya jagoranta, shi ya haifar da rikici a Mali inda Mayakan Jihadi a kasar suka samu damar karbe ikon yankin arewaci kafin Faransa ta taimaka aka kwato yankin.
Sanogo na iya fuskantar hukuncin kisa kan kisan sojoji da ya binne a wani katon kabari shake da gawarwaki sama da 30.
An dage shari’ar zuwa ranar juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu