Isa ga babban shafi
Mali

Gwamnatin Mali ta sauke Ministan tsaronta daga mukaminsa

Rundunar sojin Mali ta sanar da kwace garin Boni da ke tsakiyar kasar daga hannun ‘yan tawaye da suka karbe iko da shi na wasu sa’o’i kadan. 

Ministan tsaron Mali da aka sauke daga mukaminsa Tiéman Hubert Coulibaly
Ministan tsaron Mali da aka sauke daga mukaminsa Tiéman Hubert Coulibaly Wikimedia commons
Talla

Sai dai kuma majiyar tsaron kasar, ta shaidawa mana cewa, mayakan ‘yan tawayen sun tsere da magajin garin na Boni a matsayin garkuwa, bayan kone ofishinsa da suka yi.

Tun a jiyan dai gwamnatin kasar ta sauke Ministan tsaronta Hubert Coulibali daga mukaminsa, tare da bayyana Abdoulaye Idrissa a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Wata majiya daga ma’aikatar tsaron kasar ta ce tube Coulibalin daga mukaminsa, na da nasaba da mamaye garin Boni da ‘yan tawaye suka yi a Juma’ar da ta gabata, da kuma harin da mayakan suka kaiwa barikin sojan kasar da ke Nampala inda sojoji 17 suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.