MDD ta bukaci Jammeh ya mika mulki
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci shugaban Gambia, Yahya Jammeh da ya mika nulki ga Adama Barrow da ya yi nasara a zaben da aka gudanar a farkon watan Disamba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannna na zuwa ne bayan Jammeh ya sanar da kin amincewa da shan kayi, in da ya zargi jami’an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai.
Wata sanarwar da mambobin kwamitin 15 suka fitar, ta bukaci Jammeh da ya mutunta muradun ‘yan kasarsa kamar dai yadda ya yi a ranar 2 ga watan Disamban, in da ya amince da shan kayi.
Ministan harkokin wajen Senagal ne, Mankeur Ndiaye ya bukaci kwamitin tsaron da ya tsoma baki cikin lamarin.
A bangare guda, shugaban Jammeh ya hana jirgin shugabar kungiyar kasashen ECOWAS kuma shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirlef sauka a cikin kasarsa, yayin da ya girke jami’an tsaro akan tituna.
Zababben shugaban kasar, Adama Barrow ya yi kira ga al'ummar kasar da su kwantar da hankulansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu