Isa ga babban shafi
Gambia

'Yan adawa na murnar samun nasara a zaben Gambia

Shugaban kasar Gambia mai barin gado Yahya Jammeh, ya ce har kullum zai ci gaba da amincewa da zabin al’ummar kasar, inda ya kara jaddada dalilansu na amincewa da sakamakon zaben da ya bai wa abokin hamayyarsa Adama Barrow nasara a zaben da aka gudanar ranar alhamis da ta gabata.

Adama Barrow lokacin wani taronsa na gangami.
Adama Barrow lokacin wani taronsa na gangami. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

A wani jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar cikin daren da ya gabata, Jammeh, ya jaddada mubaya’arsa ga zababben shugaban wanda ya yi nasara da kimanin kashi 45 cikin dari na kuri’un da aka jefa.

Yahya Jammeh wanda ya share tsawon shekaru 22 kan karagar mulki, a lokacin yakin neman zabe ya ce a shirye yake ya mulki kasar har na tsawon shekaru milyan daya matukar dai Allah ya ba shi damar yin haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.