Isa ga babban shafi
Gambia

Zaben Gambia: Yahya Jammeh yaki amincewa da shan kaye

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a a satin da ya gabata, wanda abokin hamayyarsa Adama Barrow yayi nasara.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh.
Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh. AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

A wani jawabi da ya gabatar ta kafar Talabijin jiya juma’a, Jammeh ya bukaci da sake gudanar da sabon zabe, sanarwar da ake kallonta a matsayin koma baya ga cigaban dimokaradiyar kasar.

A satin da ya gabata ne dai Jammeh ya amsa shan kaye a jawabin da ya gabatar ta kafafen yada labarai, kafin daga bisani a daren Juma’a ya janye kalamansa.

Tuni dai dan takarar da yayi nasara a zaben shugabancin kasar Adama Barrow ya zargi Jammeh da yunkurin lalata tsarin Dimokaradiyya saboda kin amincewa da shan kaye.

Yahya Jammeh wanda ya dare kan mulkin Gambia bayan juyin mulkin da ya jagoranta a 1994 ya sha kaye ne zaben shugabancin kasar da ya gudana, bayan da Adama Barrow ya lashe fiye da kasha 43 na kuri’un da aka kada.

A wani jawabi da gwamnatin Amurka ta fitar, ta tur da yunkurin na Jammeh tare da bayyana shi a matsayin karantsaye ga tsarin dimokaradiyya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.