Isa ga babban shafi
Gambia

Barrow ya fara shirin karbar mulkin Gambia

Wani lokaci a yau ne zababben shugaban Gambia Adama Barrow zai gana da wata tawaga don tattaunawa kan shirin karbar mulki daga hannun shugaba Yahya Jammeh da ya sha kayi a zaben da aka gudanar a ranar Alhamis.

Zababben shugaban Gambia Adama Barrow,
Zababben shugaban Gambia Adama Barrow, STR / AFP
Talla

Mr. Barrow zai gana da shugabannin ‘yan adawa guda bakwai da suka mara masa baya har ya yi nasarar doke Jammeh da ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 22.

Ana kyautata zaton sabon shugaban zai sauya tsarin tafiyar da gwamnatin Jammeh da ya mayar da Gambia saniyar ware a tsakanin kasashen duniya.

Kazalika sabon shugaban ya lashi takobin maido da Gambia cikin kungiyar renon Ingila da kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da Jammeh ya raba gari da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.