Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Afrika ta Tsakiya zata samu tallafin Dala biliyan 2

Masu bada agaji na kasashen Duniya sun yi alkawarin tallafawa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Dala biliyan 2.2 sakamakon rikice-rikicen da ta yi fama da su.

Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadera tare da Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara
Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadera tare da Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara
Talla

Wadanda suka yi alkawarin bada agajin sun hada da kungiyar kasashen Turai, Asususn bada lamuni na duniya da bankin duniya, sai kuma Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen Faransa da Amurka.

Shugabannin jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Faustin Archange Touadera da ke magana a taron da ya gudana a birnin Brussels ya ce, za su yi amafani da tallafin don ganin shirinsu na farfado da kasar ya samu nasara.

Tallafin kudaden ya zarce Dalar Amurka biliyan 1.6 da shugaba Touadera ya bukata a baya don tada komadar tattalin arzikin kasar.

Amma tallafin bai kai Dala biliyan 3 ba, wato adadin kudaden da kasar ke bukata cikin shekaru biyar, don aiwatar da shirin nata.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na daya daga cikin kasashen Afrika masu fama da talauci, yayinda kimanin mutane miliyan biyar ke rayuwa a kasar, wadda ke fama da matsalar rarrabuwar kawuna kan banbancin addini da kabila.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.