Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta janye dakarunta a Afrika ta tsakiya

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya tabbatar da kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya na dakarun kasar a Jamhuriyyar a Afrika ta tsakiya, bayan cika shekaru uku da aikin wanzar da zaman lafiya.

Dakarun Faransa sun kammala aiki a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Dakarun Faransa sun kammala aiki a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya REUTERS/Luc Gnago
Talla

Amma Mista Le Drian ya bayyana cewa, Faransa za ta ci gaba da sa ido kan Jamhuriyar Tsakiyar Afrika duk da ta janye dakarunta a kasar da ta yi fama da rikice-rikice.

A wata hira da ya yi da RFI, Firaministan Faransa, Manuel Valls ya ce, ba za su yi watsi da sha’anin Afrika ta Tsakiya ba da suka bai wa reno.

Faransan yanzu dai ta janye dakarunta daga kasar bayan sun cika shekaru uku da aikin wanzar da zaman lafiya.

Sai dai janye dakarun na zuwa ne a dai dai lokacin da sabbin rikice-rikice ke barkewa tsakanin ‘yan tawayen Seleka na Musulmai da kuma Anti Balaka na Kirista.

Faransa ta bayyana damuwarta game da rikicin da ya lakuma rayukan mutane 25 a cikin makon jiya, inda ta ce, dole ne Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai su tsoma baki don tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Tun a cikin watan Disamban shekarar 2013 ne, Faransa ta girke dakarunta sakamkon zubar da jinin mutane da ake yi a kasar.

To sai dai duk da cewa rundunar ta taka rawa wajen kawo kawo karshen kisan kiyashi, amma ba ta yi nasarar raba ‘yan tawayen kasar da makamai ba.

Tuni dai al’ummar Afrika ta tsakiya suka fara nuna damuwa kan janyewar dakarun saboda dari darin yiwuwar ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.