Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan adawa sun yi arangama da 'yan sandan Zimbabwe

Yan sanda a Zimbabwe sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma duka da kulake a kokarinsu na watsa taron ‘yan jam’iyyar adawar kasar da ke zanga zanga a babban birnin kasar Harare.

Zanga zanga ta juye zuwa tashin hankali a Zimbabwe
Zanga zanga ta juye zuwa tashin hankali a Zimbabwe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Sama da matasa 200 daga jam’iyyar adawa ta MDC suna gudanar da zanga zangar ce game da cin zarafi da suka ce suna fuskanta daga wajen jami’an ‘yan sandan kasar.

Rahotanni sun ce da yawa daga cikin masu zanga zangar sun samu raunuka, sai dai kakakin rundunar 'yan sandan ta Zimbabwe Charity Charamba ta musanta rahoton raunata wasu daga cikin ‘yan adawar.

Zanga zangar na zuwa kwanaki biyu kafin gudanar da makamanciyarta da gamayyar jam'iyyun adawar kasar suka shirya domin tursasawa Mugabe zartas da sabbin dokokin zaben kasar kafin shekara 2018, lokacin da aka tsaida domin gudanar da babban zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.