Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan adawa a Zimbabwe sun gudanar da gangami

Gamayyar jam’iyyun adawa a Kasar Zimbabwe sun gudanar da gangamin nuna rashin gamsuwa da kokarin gwamnatin Robert Mugabe wajen farfado da tattalin arzikin kasar. 

Morgan Tsvangirai da Joice Mujuru
Morgan Tsvangirai da Joice Mujuru REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Yayin gangamin babban mai adawa da Mugabe, Morgan Tsvangirai da kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa Joice Mujuru sun bukaci dunkulewar jam’iyyun adawa a kasar don kawar da Mugabe da ya shafe kusan shekaru 30 yana mulkin kasar.

Zimbabwe na fama da tabarbarewar tattalin arziki da ya sanya gwamnatin Mugabe biyan ma’aikatan kasar albashi da kyar, lamarin da ya jawo zanga zanga a sassan kasar.

Kimanin makwanni uku da suka gabata sai da wasu magoya bayan Robert Mugabe da suka yi gwagwarmaya tare suka bayyana janye goyon bayansu ga gwamnatinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.