Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Sojin Zimbabwe sun dawo daga rakiyar Mugabe

Tsoffin zaratan sojin Zimbabwe, sun caccaki shugaban kasar Robert Mugabe kan shirinsa na yin tazarce a shekara ta 2018 duk da tsawon shekarun da ya shafe rike da madafun iko. 

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Sojojin wadanda suka fafata da turawan mulkin mallaka a shekara ta 1972-79, sun dawo daga rakiyar Mugabe da aka bayyana a matsayin shugaban kasa mafi dadewa kan karagar mulki a duniya.

Sojojin sun ce ba za su mara masa baya ba, matukar ya dage kan ci gaba da mulkin kasar yayin da suka kira shi mai mulkin kama-karya.

 

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da al’ummar Zimbabwe ke kokawa kan matsalar tattalin arzikin da suka tsinci kan su a ciki a karkashin shugabancin Mugabe mai shekaru 92.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.