Zimbabwe
An kama Pasto saboda bore a Zimbabwe
Hukumomin kasar Zimbabwe sun kama Pastor Evan Mawarire, daya daga cikin masu shirya zanga- zangar adawa da shugaba Robert Mugabe da aka shirya gudanarwa a yau, inda suke tuhumar sa da laifin tinzira jama’a.
Wallafawa ranar:
Talla
Masu zanga-zangar na bayyana damuwa kan halin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma mulkin kama-karyar da suke zargin gwamnatin kasar da yi musu.
A makon jiya an gudanar da irin wannan zanga-zangar wadda ta sa aka rufe shaguna da makarantu da kotuna da wasu ma’aikatun gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu