Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Kotun Zimbabwe na tuhumar babban mai shigar da kara

Babban mai shigar da karar na Zimbabwe ya bayyana a gaban kotun kasar da ke birnin Harare, sakamakon zargin sa da yi wa shari’a karan tsaye bayan ya yi watsi da shari’ar wasu mutane da ake zargi da kitsa kona gonar iyalan shugaba Robert Mugabe.

Babban mai shigar da karar Zimbabwe Johannes Tomana.
Babban mai shigar da karar Zimbabwe Johannes Tomana. Manicapost.com
Talla

Babban mai shigar da karan, Johannes Tomana mai shekaru 48 makusanci ne ga shugaba Mugabe da ke kan karagar mulkin kasar tun shekarar 1980.

Kuma baya ga tuhumarsa da ake yi da yi wa shari’a karan tsaye, ana kuma tuhumarsa da karya dokoki bayan bayar da umarnin sakin mutane 2 daga cikin mutane 4 da ake zargi da cin amanar kasa.

Wadanda ake zargi da kitsa kai harin bam a gonar iyalan Mugabe sun hada da shugaba kuma jigo a jami’iayar adawa ta Peoples Front, da wani jami’in soji da wani jami’in leken asirin kasar mai ritaya

Kuma an cafke su ne a kusa da gonar Mugabe da ke Mazowe a yankin yammacin kasar, inda ake tuhumarsu da shirin kai harin a wani mataki nuna adawa da mulkin Mugabe

A yanzu dai Tomana da ya bayyana gaban alkali Vakai Chikwekwe a kotun Harare, an bayar da belinsa kan dala dubu 1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.