Isa ga babban shafi

‘Yan sandan Kano sun dauki mataki akan Kwankwaso da Ganduje

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta haramta tarukan da Gwamnatin jihar ta shiya gudanarwa da kuma taron aurar da zawarawa na tsohon gwamnan Jihar Rabiu Musa Kwankwaso a karshen mako saboda barazanar tashin hankali da kan iya biyo bayan tarukan guda biyu.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da tsohon Gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da tsohon Gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso naij.com
Talla

Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya taron aurar da zawarawa ne a ranar Asabar karkashin wata gidauniyar shi yayin da kuma gwamnatin Ganduje ta shirya gudanar da wani taron matasa a Kano.

Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Magaji Majiya ya ce bukukuwan sun yi karo da juna wanda ke iya haifar da hargitsi da tashin hankali daga tarukan gudas biyu.

Wannan dai na dada fito da barakar da ke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso da kuma wanda ya gaje shi Abdullahi Ganduje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.