Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin Kano ya soki aurar da mata masu karancin shekaru

Mai martaba sarkin kano Alhaji Muhammad Sanusi na biyu ya nemi karfafa dokar hana aurar da ‘yan mata masu kasa da shekaru 18 sakamakon illolin da ke tattare da hakan a wannan zamanin.

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu
Talla

Sarkin na Magana ne a yayin wani taron karawa juna sani da aka yi jiya talata a jahar Kano.

Sarki Sunusi na biyu ya ce yakamata al’ummar musulmi su gane illar yiwa mata aure da wuri ganin yana daya daga cikin dalilan dake kai ga sukurkucewar aure da wuri ga kuma matsalar cutar yoyon fitsari da aka gaza magance shi yanzu.

Sarkin ya kuma shawarci hukumomin dasu kafa dokar hukunta masu barin ‘ya’yansu suna ta garanranba a wulakance ba tare da kulawa ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.