Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya zata tura sojoji 4,000 zuwa Sudan ta Kudu

Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya amince da sake tura rundunar wanzar da zaman lafiya da ta kunshi sojoji 4,000 zuwa kasar Sudan ta Kudu, saboda fargabar kada sabon fadan da ya barke, ya sake jefa kasar cikin yakin basasa.

Jami'an wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
Jami'an wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu Reuters
Talla

Sai dai kuma matakin ya fuskanci tirjiya daga gwamnatin Sudan ta Kudun, inda kakakin gwamnatin Ateny Wek Ateny ya ce kasar ba zata lamunci abinda ya kira mamaya daga Majalisar dinkin duniya ba.

Kafin kaiwa ga wannan matsayi majalisar dinkin duniyar ta sha zargin sojojin gwamnati na Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki ta hanyar cin zarafin fararen hula. Zargin da gwamnati ke dorawa 'yan tawayen kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.