Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu ya sauya mataimakinsa

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya sauya mataimakinsa kuma tsohon jagoran ‘yan tawayen kasar Riek Machar, abinda ke kara fito da rashin jituwaa tsakanin bangarorin biyu. 

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Stringer
Talla

Shugaba Salva Kirr ya sanar da nada Taban Deng Gai a matsayin mataimakinsa na yanzu bayan kungiyar SPLM da Machar ke jaogaranta ta ba shi shawarar aiwatar da haka.

A makon jiya ne, Riek Machar ya kori Mr. Deng daga mukaminsa na ministan albarkatun karkashin kasa, kuma da ma Machar ne ke da alhakin nada ko kuma sauke wani a mukamin.

A bangare guda, mambobin kungiyar ta SPLM da suka yi arangama da dakarun gwamnatin kasar a cikin wannan watan a Juba, sun ayyana Deng a matsayin jagoransu.

Tun dai lokacin da sabon rikicin kasar ya barke ne, Mr. Machar ya fice daga birnin Juba bayan ya yi zargin cewa shugaba Salva Kiir na shirin kashe shi.

Ko da dai gabanin daukan matakin sauya shi, sai dai Salva Kiir ya bai wa Riek Machar wa’adin sa’oi 48 da ya dawo Juba ko kuma ya sauya shi.

Sai dai ana ganin matakin zai warware yarjeniyar zaman lafiyar da aka cimma a bara, abinda zai sake jefa jinjirar kasar ta Sudan ta Kudu cikin wani yakin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.